logo

HAUSA

Masana’antar kera injuna ta Sin ta samu ci gaba a rabin farkon bana

2024-08-08 10:41:42 CMG Hausa

Masana’antar kera injuna ta kasar Sin ta samu ci gaba a rabin farko na bana, yayin da masana’antun samar da kayayyaki masu alaka da fasahohin zamani da masu kare muhalli ke kara samun karbuwa.

Kungiyar masu kera injuna ta kasar Sin (CMIF) ta bayyana a jiya Laraba cewa, masana’antar ta samu sabon kuzari daga bangarorin da suka hada da na motoci masu amfani da makamashi mai tsafta da na samar da mutum mutumin inji masu aiki a masana’antu. A cewar kungiyar, a rabin farko na bana, kerawa da sayar da motoci masu amfani da makamashi mai tsafta sun samu karuwar kaso 30.1 da kaso 32 cikin dari, daga shekara daya da ta gabata, yayin da bangaren samar da mutum mutumin inji masu aiki a masana’antu, ya karu da kaso 9.6. (Fa’iza Mustapha)