Kasar Sin na kan gaba wajen neman ikon mallakar fasaha a fannin kiyaye muhalli a duniya fiye da 50%
2024-08-07 20:38:11 CMG Hausa
Karuwar takardun neman ikon mallakar fasahohi ta nuna irin gudummawar da kasar Sin ke bayarwa wajen samun ci gaban duniya mai dorewa, kamar yadda rahoton da hukumar kula da harkokin ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ta fitar a baya-bayan nan ya nuna cewa, kasar Sin tana kan matsayi na daya a fannin yawan neman iznin ikon mallakar fasaha a fannin kiyaye muhalli da rage fitar da hayakin carbon a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 20 cikin 100 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, sama da rabin jimilla na duniya baki daya.
Karuwar ya haura da maki 7.1 cikin 100 sama da matsakaicin adadi na duniya baki daya, a cewar hukumar kula da harkokin ikon mallakar fasaha ta kasar Sin a cikin rahoton kididdigar da aka yi game da ikon mallakar fasaha a fannin kiyaye muhalli da rage fitar da hayakin carbon.
Kasar Sin ta taka rawar gani sosai a fannin adana makamashi, inda ta samu takardun neman ikon mallakar fasaha 37,000 a shekarar 2023 kadai, wanda ya kai kashi 48 cikin 100 na yawan adadi na duniya. Dangane da makamashi mai tsafta kuma, adadin takardun neman ikon mallakar fasaha a fannonin makamashin hasken rana da makamashin hydrogen ya kasance mafi yawa a duniya, inda ya kai 8,000 da 5,000, bi da bi. (Yahaya)