logo

HAUSA

Kasar Sin na son inganta musaya da hadin gwiwa da Birtaniya

2024-08-07 21:26:11 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin tana son inganta musaya da hadin gwiwa da Birtaniya.

Mao ta yi tsokacin ne a lokacin da aka tambaye ta don tabbatar da ko ministan harkokin wajen Birtaniya David Lammy zai kawo ziyara kasar Sin.

Mao ta bayyana cewa, ba da dadewa ba ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da Lammy a Vientiane, babban birnin kasar Laos.

Ta kara da cewa, kasar Sin da Birtaniya dukkansu mambobi ne na dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, inda ta kara da cewa, dangantakar moriyar juna kuma mai karko dake tsakanin Sin da Birtaniya, ta kasance tushen  muhimman muradun jama'ar kasashen biyu, kuma tana taimakawa kasashen biyu su daidaita kalubalen duniya tare, da ba da gudummawa ga zaman lafiyar duniya da ci gaban duniya. (Yahaya)