Cinikayya tsakanin Sin da kasashen ketare ya karu da kaso 6.2 a watanni 7 na farkon bana
2024-08-07 14:08:48 CMG Hausa
Jimilar darajar kayayyakin da Sin ta yi cinikayyarsu a watanni 7 na farkon bana, ta kai yuan triliyan 24.83, karuwar kaso 6.2 a kan na makamancin lokacin a bara.
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana a yau Laraba cewa, yawan kayayyakin da Sin ke fitarwa ketare ya karu da kaso 6.7 tsakanin watan Junairu zuwa Yuli, yayin da wadanda ke shigowa kasar ya karu da kaso 5.4 cikin dari. (Fa’iza Mustapha)