logo

HAUSA

Wang Yi ya tattauna da takwarorinsa na Masar da Jordan game da yanayin Gabas ta Tsakiya

2024-08-07 10:19:38 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, Sin na adawa tare da yin tir da kisan shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Iran, yana mai bayyana kisan a matsayin abun da ya kara tsananta yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, da keta ka’idojin MDD da iko da mutuncin kasar Iran, har ma da yin cikas ga kokarin ingiza zaman lafiya da dakatar da tsagaita bude wuta a zirin Gaza.

Wang Yi ya bayyana haka ne jiya Talata, yayin tattaunawa da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, da na Jordan Ayman Safadi ta wayar tarho, don gane da yanayin da ake ciki a yanyin Gabas ta Tsakiya.

Ministan na Sin ya kara da cewa, kasarsa za ta karfafa hadin kai da kasashen Larabawa, da ma dukkan bangarori domin kaucewa kara ta’azzarar yanayin da ma tabarbarewarsa.

A nasa bangare, Badr Abdelatty ya ce Masar na matukar yabawa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen ingiza zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da kokarin da take yi na sulhunta bangarori masu adawa a cikin Palasdinu.

Ya ce, Masar na fatan ci gaba da tuntuba tsakninta da kasar Sin domin kaucewa ta’azzarar yanayin.

Shi ma Ayman Safadi na Jordan cewa ya yi, ya kamata kasa da kasa su dauki mataki nan take domin kaucewa kazamcewar rikicin Gaza, da dakatar da keta dokokin kasa da kasa, da cimma tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, tare da samar da cikakken ‘yancin kan Palasdinu ta hanyar kafa kasashe biyu.

Ya ce kasar Sin ta dauki matsayi na adalci game da rikicin Palasdinu da Isra’ila, kuma a shirye Jordan take ta ci gaba da tuntuba tsakaninta da kasar Sin, kana ta yi ammana Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta dakatar da bude wuta da kawo karshen yakin. (Fa’iza Mustapha)