logo

HAUSA

Shugaban Timor-Leste Ya Yaba Kayayyaki Kirar Kasar Sin

2024-08-07 15:54:28 CMG Hausa

Shugaban kasar Timor-Leste Jose Manuel Ramos-Horta ya ziyarci kasar Sin daga ranar 28 zuwa 31 ga watan Yulin da ya gabata. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Timor-Leste ya ziyarci kasar Sin tun bayan kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

A wata hira ta musamman da ya yi da babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Ramos-Horta ya godewa kayayyaki kirar kasar Sin da suka ba yaran kasarsa damar samun takalma don fita da jakunkuna don zuwa makaranta.

Ramos-Horta ya ce, a duniya, za a iya samun kimanin mutane biliyan biyu zuwa uku, wadanda suke iya kasahewa dala biyu zuwa biyar kawai a rana, yayin da masana’antu a kasar Sin ke samar da kayayyaki masu fasahar zamani, har ma da samar da kayayyakin da wadannan mutane za su iya saye. A cewarsa, Sinawa ne kawai za su iya baiwa talakawan duniya kayayyakin da za su iya saye, kuma wannan ita ce hikimar da kasar Sin ke da ita. (Bilkisu Xin)