logo

HAUSA

Xi ya nanata bukatar kare al’adu da kayayyakin gargajiya na kasar Sin

2024-08-06 14:15:36 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci a kara kokarin kare al’adu da abubuwa masu daraja tare da sabunta kyawunsu a sabon zamani

Xi ya yi kiran ne cikin umarnin da ya bayar na karfafa karewa da kulawa da amfana daga al’adu da kayayyakin gargajiya na kasar.

Hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO), ta sanar da sanya ginin da ya raba birnin Beijing da hamadar Badain Jaran da yankin kiyaye tsuntsaye masu kaura, wanda ke kusa da gabar rawayen teku da tekun Bohai, cikin jerin kayayyakin gargajiya na duniya da aka yi gado. UNESCO ta bayar da sanarwar ce yayin taro na 46 na kwamitinta mai kula da kayayyakin da aka yi gado, wanda ya gudana a birnin New Delhi na Indiya.

A cewar shugaba Xi Jinping, sanya wadannan kayayyaki cikin jerin na UNESCO na da muhimmanci ga aikin zamanantar da kasar Sin, wanda zai kunshi ci gaban da aka samu ta fuskar al’adu da kayayyakin gado da jituwa tsakanin bil Adama da sauran halittu, lamarin da zai kara haskaka wayewar kan duniya. (Fa’iza Mustapha)