logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi nasarar harba sabbin taurarin dan Adam

2024-08-06 20:31:14 CMG Hausa

A yau Talata ne kasar Sin ta harba wani sabon rukunin taurarin dan Adam zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin.

Taurarin na dan Adam 18 su ne rukunin farko na tsarin taurarin dan Adam mai suna Spacesail Constellation, wanda zai samar wa masu amfani da intanet na duniya hidimar intanet mai saurin gaske da karko da inganci, a cewar kamfanin da ya harba taurarin wato China Great Wall Industry Corporation.

An harba rukunin taurarin dan Adam din ne da karfe 2 da mintuna 42 na rana, agogon Beijing, a cikin wani rokar dakon kaya na Long March-6 da aka gyara kuma ya shiga falakinsa cikin nasara.

Wannan shi ne aiki na 530 da rokar dakon kaya na Long March ta yi. (Yahaya)