logo

HAUSA

An kammala aikin ficewar sojojin Amurka daga Agadez na jamhuriyar Nijar

2024-08-06 10:23:24 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, a ranar jiya ne 5 ga watan Augustan shekarar 2024 aka yi bikin kammala aikin ficewar sojojin Amurka daga Nijar, a sansanin sojojin sama mai lamba 201 da ke Agadez. Bikin ya gudana a gaban idon babban jami’in sojojin Amurka na AFRICOM Kenneth P. Ekman da kuma na sojojin Nijar kwamandan Ibrahim Talba na sansanin sojan 201. 

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba wannan sanarwa ga kuma rahoton da ya aiko mana.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, ma’aikatar tsaron kasar Amurka da ma’aikatar tsaron kasar Nijar suka sanar da cewa aikin janye sojojin Amurka da kayayyakinsu daga sansanin soja mai lamba 201 dake Agadez ya kammala.

Aikin da aka fara a ranar 19 ga watan Mayu bayan da aka cimma yarjejeniya da matakan janye sojoji da kuma ci gaba da kula da aikin tsakanin rundunonin kasashen biyu, har nan da tsawon makwanni masu zuwa domin tabbatar da cewa aikin janye sojojin ya kare baki daya kamar yadda aka tsara. (Mamane Ada)