logo

HAUSA

Gwamnatin tarayya ta raba naira biliyan 570 ga gwamnonin kasar domin su taimakawa al’umominsu

2024-08-06 10:47:36 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da sakin tsabar kudi har naira biliyan 570 ga jihohin kasar 36 ciki har da Abuja domin su taimakawa al’umominsu wajen rage radadin rayuwa.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasar Alhaji Muhammed Idris ne ya tabbatar da hakan da yake zantawa da manema labarai a karshen makon jiya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan ya ce, hakika gwamnonin jihohin na sanar da shugaban kasa halin da al’umominsu ke ciki na tsadar rayuwa, wannan ce ta kara baiwa gwamnati kwarin gwiwar fito da tsare-tsare da dama da talaka zai amfana kama daga tallafin kudi kai tsaye ga ’yan kasa da samar da kayan abinci domin rabawa kyauta ga jama’a.

Ministan ya ce, an rabawa gwamnatocin jihohi wadannan kudade ne a tsakanin karshen watan Yuli na 2023 zuwa 2024, kuma an kasafta kudaden ne a tsakanin kowacce jiha karkashin shirin tallafin bankin duniya.

Ministan ya ce, har yanzu gwamnatin tarayyar ba ta nuna gajiyawa ba wajen taimakawa manufofin gwamnatocin jihohi da suke da nasaba da tallafin rayuwar al’umma, kama daga shawarwari da kuma na kudade.

Alhaji Muhammad Idris ya ci gaba da nuna bukatar jama’a da su kara baiwa gwamnatoci a dukkan matakai a hadin kan da ya kamata domin samar da sahihiyar mafita ga kasa baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)