logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Borno za ta hana amfani da takin urea saboda amfani da shi da ‘yan ta’adda ke yi wajen hada Bom

2024-08-04 16:31:44 CMG Hausa

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatin jihar na duba yiwuwar dakatar da amfani da taki mai sinadarin Urea a duk fadin jihar, sakamakon gano cewa ‘yan ta’adda na amfani da shi a matsayin sinadarin hada bama-bamai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne ranar Juma’ar da ta gabata 2 ga wata lokacin da ya kai ziyarar duba mutanen da suke kwance a asibiti dake birnin Maiduguri sakamakon raunukan da suka samu bayan harin bom da aka kai a yankin Kawuri ranar Larabar da ta gabata, ya ce yanayin kasar Borno ba sai lallai manoma sun yi amfani da takin urea ba wajen noma abinci.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahato.

 

Farfesa Babagana Umara Zulum ya nanata kudurin gwamnatin jihar na daukar dukkan matakan da suka kamata wajen kawo karshen hare-haren bama-bamai a jihar baki daya, inda ya yi alla wadai da harin da aka kai yankin Goza da Konduga.

Harin na Kawuri wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ya faru ne tsakanin wata guda kacal da harin da ya faru a yankin Goza.

Ya ce ko da a ranar da aka fara zanga-zanga, an samu rahoton tashin bom a garin Maiduguri, inda bincike ya tabbatar da cewa kayayyakin hada bom din ba su da wahalar samuwa.

“Idan har amfani da takin zai cigaba da haifar mana da wannan matsala, to muna ganin akwai bukatar gwamnatin jihar Borno ta sake duba manufofinta ta fuskar amfani da takin Urea a jihar, kasancewar dai muna da wata mafita ta daban.”

A kan batun zanga-zanga kuwa da yake gudana a duk fadin kasar wanda yau Lahadi aka shiga rana ta 4, gwamnan na jihar Borno ya sanar da dage dokar hana zirga-zirga da ya kafa.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci da a kara sanya ido sosai a kan mutanen da suke amfani da kananan yara wajen haddasa fitina a jihar don kawai biyan bukatun kai.

“Sama da kaso 90 na masu zanga-zangar kananan yara, wannan abin takaici ne mutuka, kuma da yawansu ba su da iyaye a wannan jihar sannan kuma ba su da masu kula da su, wajibi ne mu yi wani abu mai karfi a kan wannan.” (Garba Abdullahi Bagwai)