Wasu mahara sun kai hari otal din Lido Beach dake birnin Mogadishun kasar Somalia
2024-08-03 17:38:17 CMG Hausa
A kalla mutane 31 sun rasu, kana wasu 61 sun jikkata, bayan da wasu mahara suka kai hari kan sanannen otal din Lido Beach dake bakin ruwa, a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somalia.
‘Yan sanda da shaidun gani da ido, sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an tayar da wani abun fashewa a kusa da otal din, da wani wurin cin abinci dake daura da shi, a kusa da wasu gine-ginen jami’an tsaron gwamnati dake birnin.
Wadanda suka shaida faruwar harin, sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam a kusa da otal din na bakin ruwa, bayan da maharan suka bude wuta kan otal din. Kaza lika, wasu shaidun sun ce yayin harin, jami’an tsaro sun hallaka wasu daga ‘yan bindigar, ana kuma gudanar da ayyukan ceto. (Saminu Alhassan)