logo

HAUSA

Kudurin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shafi manyan tsare-tsare tare da matakai na zahiri

2024-08-03 17:05:13 CMG Hausa

Kudurin mai kalmomi dubu 22, dake kunshe da matakan yin gyare-gyare na zahiri guda 300, ya shafi fannoni daban-daban na mulkin kasa, ya kuma tsara taswirar ci gaba da zurfafa yin kwaskwarima a gida daga dukkan fannoni, da daukaka ci gaban zamanantarwa irin ta kasar Sin.

Ana iya ganin cewa a cikin kudurin, akwai manyan tsare-tsare daga fannoni da dama, akwai kuma matakan zahiri da za’a dauka. Kaza lika, abu mai muhimmanci a nan shi ne, ba batun yin gyare-gyare a harkokin mulkin kasa kawai kudurin ya mayar da hankali a kai ba, har ma da tsara manyan tsare-tsaren da suka shafi kara bude kofar kasar ga kasashen ketare, ciki har da fadada bude kofa a fannin tsari, da zurfafa yin kwaskwarima ga tsarin cinikin waje, da zurfafa yin gyare-gyare ga tsarin zuba jari na baki ’yan kasuwan waje, da na daidaita harkokin zuba jari ga kasashen waje, da kyautata tsarin bude kofa a yankuna daban-daban, da ci gaba da inganta aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” tare, al’amuran da suka samar da babban zarafi ga zuba jarin waje, gami da na sassan kasa da kasa.

Akwai yakinin cewa, manufar kasar Sin ta fannin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a sabon zamanin da muke ciki, za ta kaddamar da sabon mataki na raya al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce: “Idan duniya ta zama mai kyau, kasar Sin za ta yi kyau. Idan kasar Sin ta zama mai kyau, duniya za ta kara yin kyau.” (Murtala Zhang)