logo

HAUSA

Angola ta karbi bakuncin taron zaman lafiya na DRC

2024-07-31 10:21:27 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Angola a jiya Talata ta karbi bakuncin taron ministoci karo na biyu kan tsaro da zaman lafiya a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo (DRC) a birnin Luanda fadar mulkin kasar Angola, kuma taron ya samu halarcin ministocin harkokin wajen DRC da Rwanda.

A cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ministan harkokin wajen Angola Tete Antonio yana da yakinin cewa bangarorin za su cimma matsaya guda a yayin ganawar, tare da samar da shawarwari na hakika da nufin maido da zaman lafiya da kuma tsagaita wuta a gabashin DRC.

Taron dai ya dauki kusan sa'a guda, amma ba a fitar da wani bayani a hukumance kan sakamakon ba.

Taron na ranar Talata ya biyo bayan zaman ministocin da aka gudanar a ranar 21 ga watan Maris a birnin Luanda, inda wakilan suka amince da wajibcin samar da zaman lafiya mai dorewa a gabashin DRC, tare da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a.  Yarjejeniyoyin da aka cimma sun hada da daina rikici da juna, da aiwatar da tsagaita bude wuta, da janye dakaru. (Yahaya)