Sin ta bukaci Amurka da ta janye makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango daga Philippines bisa ga alkawarin da ta yi
2024-07-31 20:27:06 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya mayar da martani game da girke tsarin makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango da Amurka ta yi a kasar Philippines, a gun taron manema labarai da aka saba yi a yau Laraba 31 ga watan nan, inda ya bukaci kasar da abin ya shafa da ta fuskanci muryoyin kasashen yankin, ta gaggauta gyara munanan ayyukansu, da kuma janye tsarin makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango, kamar yadda ta yi alkawari a baya a bainar jama’a.
An kuma bayyana cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya sanar da cewa, kasarsa za ta baiwa Philippines dalar Amurka miliyan 500 domin karfafa tsaron ta. Game da wannan batu, Lin Jian ya yi nuni da cewa, Amurka ba ta cikin batun tekun kudancin kasar Sin, don haka, ba ta da hurumin tsoma baki a harkokin teku tsakanin Sin da Philippines.
Kaza lika, a yau Laraba, an kashe shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniya a wani hari a Iran. Game da haka, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin na adawa, da kuma yin Allah wadai da kisan gilla. Tana kuma matukar damuwa kan tsanantar rashin zaman lafiya a yankin sakamakon faruwar lamarin. (Bilkisu Xin)