Jakadan musamman na shugaban kasar Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Mauritania
2024-07-31 21:21:32 CMG Hausa
Jakadan musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin mista Wang Guangqian, zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Cheikh Ghazouani, wanda zai gudana a gobe Alhamis 1 ga watan Agusta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana hakan a Larabar nan, inda ya ce Wang Guangqian wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin, zai halarci bikin da za a gudanar a birnin Nouakchott fadar mulkin Mauritania bisa gayyatar shugaban kasar. (Saminu Alhassan)