logo

HAUSA

An kaddamar da shirin “Sabon Zamani da Sabon Fim” karo na 2

2024-07-30 15:59:55 CMG Hausa

Yau Talata, an kaddamar da shirin hadin gwiwar Sin da kasashen waje mai taken “Sabon Zamani da Sabon Fim” karo na biyu a birnin Changsha na lardin Hunan. Masana da masu nazari da kuma darektoci daga kasashen duniya sun halarci taron na wannan karo.

Hukumar harsunan waje ta kasar Sin da cibiyar shirye-shiryen labaran gaskiya da na talabijin da fina-finai na Babban Gidan Rediyo da Talabijin na kasar Sin wato CMG da wasu hukumomin sun tsara wannan shiri cikin hadin gwiwa, domin sa kaimi ga mutanen kasa da kasa da su gabatar da shirye-shiryen labaran gaskiya da gajerun bidiyoyin da suka dauka, inda za a ba da taimako gare su wajen kyautata da yada shirye-shiryensu. Kana, za su sami damar nuna shirye-shiryen da aka zaba ta manyan kafofin watsa labarai na kasar Sin da na kasashen duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)