Sin da Afrika sun himmatu wajen karfafa hadin gwiwar dijital
2024-07-30 10:42:09 CMG Hausa
Ministan masana’antu da fasahar sadarwa na kasar Sin Jin Zhuanglong ya bayyana a jiya Litinin cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannin fasahar dijital, tare da taimaka musu wajen gina dandalin fasahar dijital ta Afirka ko “Digital Afrika”
Jin ya shaidawa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa na dijital tsakanin Sin da Afirka cewa, za a tallafa wa kamfanoni ta hanyar hadin gwiwa a aikace a fannonin sadarwa ta wayar salula, da cibiyoyin bayanai, da igiyoyin sigina na karkashin ruwa da kasa.
Jin ya kara da cewa, za kuma a yi kokarin hadin gwiwa don bunkasa amfani da fasahohin zamani irin su 5G, 6G, da tsaro na cibiyoyin sadarwa, da kara ingancin aikin manyan kwamfutoci da sadarwa bisa bayanan lissafi.
A yayin taron, an fitar da shirin aikin raya hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin dijital, wanda ma'aikatar masana'antu da fasahar sadarwa ta dauki nauyin shiryawa. (Mohammed Yahaya)