Kasar Sin na adawa da danyen aikin tsoma bakin Japan da Amurka a harkokin cikin gidanta
2024-07-30 21:42:22 CMG Hausa
Dangane da sanarwar hadin gwiwa ta taron diflomasiyya da tsaro na kasashen Japan da Amurka ko 2+2, wanda ya zargi kasar Sin da manufofinta na diflomasiyya, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Lin Jian, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka saba yi a yau Talata 30 ga watan nan cewa, kasashen Japan da Amurka sun yi katsalandan cikin harkokin cikin gidan kasar Sin kan batutuwan Taiwan, da Hong Kong, da Xinjiang da Xizang, kuma sun bata sunan kasar Sin kan batutuwan da suka shafi teku, da haifar da fadace-fadace a tsakanin sassa daban daban, ta yadda hakan ya yi mummunar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, don haka kasar Sin na kakkausar adawa da hakan.
Kaza lika, game da yadda kungiyar da ake kira wai “Kungiyar ’yan majalisar dokoki mai kula da tsara manufofi kan kasar Sin” ta gudanar da taro a Taiwan, jami’in ya bayyana cewa, kasar Sin ta shawarci ’yan majalisar da abin ya shafa da su daina amfani da batun Taiwan wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin guda daya ce tak a duniya, kana Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya ware shi ba, yayin da batun Taiwan ke matsayin harkar cikin gida ta Sin kadai, kuma ba za a yarda wani karfi na waje ya tsoma baki a cikinsa ba. (Bilkisu Xin)