Ministan wajen kasar Zambia zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin
2024-07-30 21:33:27 CMG Hausa
Ministan ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Zambia Mulambo Haimbe, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, tun daga yau Talata har zuwa Juma’a biyu ga watan Agusta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ne ya sanar da hakan a Talatar nan, inda ya ce mista Haimbe, zai ziyarci Sin ne bisa gayyatar da takwaransa na kasar Sin Wang Yi ya yi masa.