logo

HAUSA

Kasar Sin ta kaddamar da martanin gaggawa kan ambaliyar ruwa a yankin Beijing-Tianjin- Hebei

2024-07-30 10:19:17 CMG Hausa

A jiya Litinin ne hedikwatar yaki da ambaliyar ruwa ta kasar Sin ta kaddamar da mataki na hudu na martanin gaggawa ga ambaliyar ruwa a yankin Beijing-Tianjin-Hebei, bisa hasashen cewa za a yi ruwan sama mai tsanani da yiwuwar ambaliyar ruwa.

Ma’aikatar ba da agajin gaggawa ta kasar (MEM) ta sanar da cewa, daga ranar Litinin zuwa Talata ana hasashen za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin, lamarin da ka iya haifar da ambaliyar ruwa.

A sa’i daya kuma, ma’aikatar ta agajin gaggawa ta yi aiki tare da ma’aikatar masana’antu da sadarwa wajen aika da jiragen sama mara matuka zuwa lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, don tallafawa ayyukan agaji na cikin gida.

Kazalika, ma’aikatar da hukumar kula da tanadin abinci da tsare-tsare ta kasar Sin sun kuma ware kayayyakin agaji da darajarsu ta kai Yuan miliyan 4.41, kwatankwacin dalar Amurka 618,000 ga lardin Liaoning na arewa maso gabashin kasar Sin. (Mohammed Yahaya)