An kaddamar da atisayen soja mai taken “Hadin gwiwa da zaman lafiya na 2024”
2024-07-30 10:55:58 CMG Hausa
Da safiyar Jiya Litinin, rundunonin sojojin kasashen Sin da Tanzaniya da kuma Mozambique sun kaddamar da atisayen soja mai taken “Hadin gwiwa da zaman lafiya na shekarar 2024” a kasar Tanzaniya.
Atisayen hadin gwiwa da aka gudanar a wannan karo ya mai da hankali kan daukar matakan soja domin yaki da ta’addanci cikin hadin gwiwa. Kana, atisayen da za a yi kan kasa, zai hada ayyukan tsara matakan soja cikin hadin gwiwa, da aikin bincike da sa ido, da kuma aikin ceto da kai hari ba zato ba tsammani da dai sauransu. Game da atisayen da za a yi a kan teku kuma, rundunonin sojoji za su yi gwajin harba bama-bamai, da aikin ceto na hadin gwiwa, da kuma yaki da ’yan ta’adda da ’yan fashin teku da dai sauransu, a yankin teku dake tashar jiragen ruwa ta Dar es Salaam.
Labarin da aka samu ya nuna cewa, za a gama atisayen kan teku zuwa ranar 5 ga watan Agusta, yayin da atisaye na kasa zai kai ranar 11 ga watan Agusta. (Mai Fassara: Maryam Yang)