Shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Timor-Leste
2024-07-29 16:23:54 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Timor-Leste Jose Ramos-Horta dake ziyarar aiki a kasar ta Sin, a birnin Beijing, fadar mulkin Sin, a yau Litinin.
Xi ya ce, kasar Sin a shirye take ta karfafa alaka da dabarun raya kasa da kasar Timor-Leste, da kuma taimaka mata wajen samun 'yancin kai na tattalin arziki da bunkasuwa a fannoni daban daban.
A nasa bangare, Ramos-Horta ya ce, Timor-Leste yana goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ke yi na kare ikon mallakar kasa da cikakken yankinta.
Bayan tattaunawar, shugabannin kasashen biyu sun shaida rattaba hannu kan shirin hadin gwiwa kan aikin gina "shawarar ziri daya da hanya daya" tare da wasu takardun hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin aikin gona, da kiyaye muhalli, da tattalin arzikin dijital, sufurin jiragen sama, da dai sauransu, bangarorin biyu sun fitar da "sanarwar hadin gwiwa na jamhuriyar jama'ar kasar Sin da jamhuriyar dimokaradiyyar Timor-Leste kan zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare". (Yahaya)