logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gana da takwararsa ta kasar Italiya

2024-07-29 10:38:26 CMG Hausa

Jiya Lahadi, a birnin Beijing na kasar Sin, firaministan kasar Sin Li Qiang ya tattauna da takwararsa ta kasar Italiya Madam Giorgia Meloni, dake ziyarar aiki a Sin, inda shugabannin biyu suka sha alwashin inganta hadin gwiwar kasashensu yadda ya kamata.

Yayin ganawar, mista Li ya yi kira ga bangarorin kasashen biyu da su ci gaba da fadada cudanyar cinikayya tsakaninsu, da karfafa hadin gwiwa a fannonin da suka hada da kera jiragen ruwa, da jiragen sama, da sabbin makamashi, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, da kuma harkokin kanana da matsakaitan kamfanoni.

A cewar babban jami'in Sin, kariyar ciniki ba za ta iya samar da karfin takara ba, kana ta hanyar bude kofa da hadin gwiwa ne za a iya tabbatar da moriyar dukkan bangarori. Saboda haka ana fatan kungiyar kasashen Turai ta EU za ta kalli ci gaban kasar Sin bisa sanin ya kamata, da ci gaba da kallon bangaren Sin a matsayin abokin hulda, da tsayawa kan yin shawarwari da hadin gwiwa don sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da EU, don tinkarar kalubalolin kasa da kasa a hadin gwiwarsu.

A nata bangare, Madam Meloni ta bayyana cewa, Italiya ta himmatu wajen raya dangantakar da ke tsakaninta da kasar Sin cikin dogon lokaci,  kuma tana son zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da masana'antu, da kimiyya da fasaha, da al'adu, da dai sauransu. Meloni ta ce Italiya a shirye take ta taka rawar gani a cikin tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin EU da Sin, don neman karfafa dangantakar hadin gwiwa a tsakaninsu. (Bello Wang)