Shugaban kasar Sin ya aike da sakon jaje ga takwaransa na Habasha
2024-07-27 22:54:32 CMG Hausa
A ran 26 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike wa takwaransa na kasar Habasha Sahle-Work Zewde wani sako, inda ya ce, ya yi matukar damuwa da samun labarin cewa, bala'in zaftarewar kasa da malalar tabo da ya auku a kwanan baya a kudancin kasar Habasha ya haddasa mutuwar mutane masu dimbin yawa tare da asarar dimbin dukiyoyi.
Shugaba Xi Jinping ya ce, a madadin gwamnati da al'ummar Sinawa, ya mika ta'aziyarsa ga kasar da iyalan wadanda suka rasu cikin bala'in, sannan ya jajantawa wadanda suka ji raunuka. Shugaba Xi yana da yakinin cewa, bisa jagorancin shugaba Sahle-Work Zewde, ba shakka gwamnati da al'ummar Habasha za su ci nasarar shawo kan bala'in, tare da sake gina gidajensu. (Sanusi Chen)