logo

HAUSA

Me ya sa manyan shugabannin kamfanonin Amurka ke ziyaratar Sin a wannan lokaci?

2024-07-26 11:20:15 CMG Hausa

 

Bayan ’yan kwanaki da kasar Sin ta rufe cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwamins ta Sin karo na 20, manyan shugabannin kamfanonin Amurka, ciki hadda FedEx da Goldman Sachs da Apple da kuma Boeing da Micron Technology da sauransu, sun kawo ziyara nan kasar Sin. Manazarta na ganin cewa, ziyarar kungiya mai kunshe da manyan shugabannin kamfanonin Amurka a daidai wannan muhimmin lokaci, na bayyana bukatarsu ta fahimtar manufofin da Sin za ta dauka wajen zurfafa yin kwaskwarima, da zummar neman samun damammakin kara hadin kai da takwarorinsu na kasar Sin.

Wannan babban taro ya gabatar da tafarkin tsarin yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga waje, wanda ya bayyana niyyar Sin ta habaka bude kofarta ga duniya. Yawan GDPn Sin a rabin farkon shekarar nan ya kai fiye da dala tiriliyan 8.5, wanda ya karu da kashi 5.0%, matakin da ya jawo ziyarar wasu manyan shugabannin masana’antu da kasuwanci. Shi ma asusun IMF ya daga hasashen da ya yi kan saurin ci gaban tattalin arzikin Sin a bana. Yana ganin cewa, kasashe da yankuna masu tasowa kuma masu karfin tattalin arziki a Asia ciki hadda kasar Sin, muhimman karfi ne dake taka rawar gani ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Har ila yau, babban taron ya nanata niyyar Sin na tsayawa kan cimma burin raya tattalin arziki da al’umma a wannan shekara, wani karin dalili ke nan da ya sa shugabannin kamfanonin ketare suka samu karin kwarin gwiwar hadin kai da kasar Sin. (Amina Xu)