An yi taron tattaunawar karshe a Cotonou tsakanin Nijar da Benin domin sake bude iyaka da maido da aikin bututun mai
2024-07-25 10:06:05 CMG Hausa
Wata tawagar manyan jami’ai ta kwamitin ceton CNSP na kasar Nijar na birnin Cotonou tun jiya Laraba domin tattaunawa tare da hukumomin Benin. Wannan tattaunawa na kasancewa a matsayin ta karshe domin neman bakin zaren kawo karshen rikici tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna, haka kuma na burin sake bude iyaka ta kasa da aka rufe tun yau da ’yan watanni da kuma ceto layin bututun mai tsakanin Nijar da Benin.
Tawagar Nijar na karkashin jagorancin birgadiye janar Mohamed Toumba, ministan cikin gida. Wannan tattaunawa ta karshe ta biyo bayan tayin goron shiga tsakani da tsoffin shugabannin kasar Benin Nicephore Soglo da Boni Yayi suka kaddamar, da kuma wannan yunkuri ya kawo su a birnin Yamai a ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata. Manyan mutanen biyu sun kira tattauna mai fa’ida tsakanin kasashen biyu domin samun mafita mai dorewa kan wannan rikici. (Mamane Ada)