logo

HAUSA

Sojojin Sin za su je Afirka don gudanar da hadin gwiwar atisaye

2024-07-25 19:54:48 CMG Hausa

 

A yammacin yau, ma'aikatar tsaron kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, babban kanar Zhang Xiaogang, mataimakin shugaban ofishin yada labarai na ma'aikatar, kuma kakakin ma'aikatar, ya ce, daga karshen watan Yuli zuwa tsakiyar watan Agusta, sojojin kasar Sin za su gudanar da hadin gwiwar atisaye mai taken "Zaman lafiya da hadin kai-2024", tare da sojojin kasashen Tanzaniya da Mozambique, wanda jigonsa shi ne "Aikin hadin gwiwa na yaki da ta'addanci" a kan doran kasa da teku. Atisayen na da nufin inganta ayyukan yaki da ta'addanci ta hadin gwiwa, da zurfafa amincewar juna da hadin gwiwar soja, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya.

Bugu da kari, game da yada kalaman tayar da yaki da "Sanarwar taron kolin Washington" da NATO ta yi, tare da yin zargi mara tushe ga kasar Sin, Zhang Xiaogang ya ce, takardar tana cike da karairayi, nuna bambanci, da kuma batanci ga kasar Sin, kuma Sin tana adawa da hakan sosai.(Safiyah Ma)