logo

HAUSA

Ministocin ma’aikatu a Najeriya sun gudanar da wani taron gaggawa tare da sakataren gwamnatin tarayya game da batun zanga-zanga

2024-07-25 10:20:05 CMG Hausa

Taron ministocin ma’aikatu a tarayyar Najeriya ya yi kira ga masu kokarin shirya zanga-zanga a kasar da su sauya shawara domin dorewar zaman lafiyar kasa da ci gabanta.

Taron wanda sakataren gwamnatin tarayya ya kirawo a ofishinsa jiya Laraba a birnin Abuja, an kuma tattauna a kan sauran batutuwan da suka shafi kasa tare kuma da jaddada goyon bayan ga shirin fadada hanyoyin bunkasar tattalin arziki da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bullo da su.

Daga tarayya Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Taron na jiya Laraba an shafe sama da sa’o’i 7 ana gudanar da shi a wani zaman na sirri domin tattauna halin da kasa ta tsinci kanta a ciki musamman yunkurin da wasu ke yi na yi wa gwamnati bore.

Ko da yake wannan ba shi karo na farko ba da gwamnati ta yi irin wannan zama a kasa da mako guda domin lalubo hanyoyi na dakatar da zanga-zangar da ’yan kasa za su gudanar a watan gobe.

A ganawar da ya yi da manema labarai bayan fitowarsu daga taron, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasar Alhaji Muhammad Idris ya ce, taron nasu ya kara hakurkurtan da masu yunkurin shirya wannan zanga-zanga.

“Ina ganin abu ne da ya kamata mu zauna gaba dayan mu tattauna domin in kuka duba za ku ga cewa zaman namu ba mu gudanar da shi ba a babban dakin taron majalissar zartarwa ta kasa dake fadar shugaban kasa, mun yi shi ne a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, kuma mun tattauna batutuwan da suka shafi kasa, kasancewar dukkanninmu muna yi wa Najeriya aiki ne, kuma muna da kyakkyawan fatan cewa Najeriya za ta bunkasa muddin dai aka sanya hakuri, a don haka muke kira ga masu niyyar zanga-zanga da su yi hakuri sosai”. (Garba Abdullahi Bagwai)