logo

HAUSA

AU ta jajantawa Habasha dangane da ibtila’in zaftarewar kasa

2024-07-24 11:22:46 CMG Hausa

Shugaban hukumar (AU) Moussa Faki Mahamat, ya mika sakon jaje dangane da mummunan ibtila’in zaftarewar kasa da ya aukawa kudancin kasar Habasha.

A cewar hukumomin yankin, zuwa yanzu, ibtila’in da ya auku a gundumar Geze Gofa dake kudancin kasar Habasha da misalin karfe 10:00 na safiyar jiya Litinin agogon wurin, ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 229, yayin da aikin ceto ke ci gaba da wakana.

Adadin mamata, wanda da farko aka ce 20 ne, ya karu cikin sauri saboda karin hadari da ya rutsa da mutanen da suka je aikin ceto.

Ibtila’in ya rutsa da malamai da ma’aikatan jinya da masana aikin gona, wadanda suka je wurin domin ceto. (Fa’iza Mustapha)