logo

HAUSA

Nijeriya ta zargi Meta da nuna wariya, tare da tilasta mata biyan tarar dala miliyan 220

2024-07-24 11:01:52 CMG Hausa

Hukumar FCCPC mai kula da takara da kare masu sayayya ta Nijeriya, ta ce tarar dala miliyan 220 da ta ci manyan kamfanonin fasaha na Meta da Whatsapp, ta biyo bayan wasu laifuffukan nuna wariya da wadanda suka cancanci hukunci da kamfanonin suka aikata.

Yayin wani taron manema labarai a Abuja babban birnin kasar, mukaddashin shugaban hukumar Adamu Abdullahi, ya ce an yanke hukunci kan kamfanonin ne bayan bincike mai zurfi da ya dauki shekaru 3.

Adamu Abdullahi ya kara da cewa, an samu dandalin Meta da laifin hana ‘yan Nijeriya ‘yancin da suke da shi na gudanar da harkoki cikin ‘yanci da yayatawa da raba bayanan mutane ba tare da izini ba.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a nasa martani game da zargin keta dokokin sirranta bayanai, dandalin Whatsapp ya lashi takobin cewa uwar kamfanin zai daukaka kara dangane da tarar, yana cewa bai amince da matakin hukumar ta FCCPC ba. (Fa’iza Mustapha)