logo

HAUSA

Bola Ahmed Tinubu: Ecowas ta samu nasarori da dama ta fuskoki daban daban

2024-07-22 09:56:05 CMG Hausa

Shugaban kungiyar Ecowas, kuma shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa taron tsakiyar shekara na kungiyar tarayyar Afrika karo na 6 cewa kungiyar Ecowas ta taimakawa mambobin kasashe wajen cimma burikansu na ci gaba ta fuskoki daban daban.

A jawabin da ya gabatar jiya Lahadi 21 ga wata a wajen taron shugaban kungiyar tarayyar Afrika a birnin Accra ta kasar Ghana, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, yana alfahari da jerin nasarorin da kungiyar ta samu a tsawon shekara guda da ya yi a matsayin shugaban kungiyar ta Ecowas.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban Mr Ajuri Ngelale wanda kuma aka rabawa manema labarai a birnin Abuja, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, kungiyar ta taimakawa kasashe shida wajen sanya hannun kan yarjejeniyar samun tallafin kamun kiwon kifi da kungiyar cinikayya ta duniya WTO, haka kuma kasashe 13 sun samu nasarar sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayya mara shinge a tsakanin kasashen Afrika.

Ta fuskar ayyukan jin kai kuwa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa taron kungiyar ta AU cewa, kungiyar ta Ecowas ta samu nasarar kashe dala miliyan 9 wajen tallafawa ’yan gudun hijira da mutanen da wani bala’i ya yi sanadin rasa muhallansu da kuma masu neman mafaka.

Haka kuma nasarorin kungiyar ya hada da tallafawa kasashen da suke gaba-gaba wajen yaki da ayyukan ta’addanci da gudummawar dala miliyan 4 karkashin shirin Ecowas na yaki da ta’addanci, yayin da kuma kungiyar ta kara karfafa shirinta na tallafawa hakokin kiwon lafiya, inda karkashin wannan shiri ake tallafawa mata masu fama da ciwon yoyon fitsari tare kuma da karfafa gwiwar mata wajen shiga sana’ar aikin noma da kuma samar musu da ingantaccen ilimi.

Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya kara da cewa, a dai cikin shekara guda kacal a matsayinsa na shugaban kungiyar ta Ecowas, an samu nasarar tallafawa kwararru daga mambobin kasashe zuwa manyan tarukan duniya domin tattaunawa a kan batutuwan da suka shafi muhalli, sannan kuma an taimakawa mambobin kasashe wajen aiwatar da yarjejeniyar Paris. (Garba Abdullahi)