logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta ci wa kamfanin Meta tarar dalar Amurka miliyan 220

2024-07-21 14:55:49 CMG Hausa

A jiya Asabar, hukumar kula da takarar kasuwanci da kare hakkin masu sayayya ta tarayyar Najeriya ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, ta hanyar gudanar da binciken hadin gwiwa na tsawon watanni 38, tare da hukumar kare bayanan jama'a ta Najeriya, ta gano cewa kamfanin Meta na kasar Amurka, wanda ke mallakar manhajar sada zumunta ta Facebook, ya yi ta keta dokoki da wasu ka'idoji na kasar Najeriya. Kana laifukan kamfanin sun hada da satar bayanan jama'a ba tare da samun izini daga wajensu ba, da nuna bambanci ga 'yan Najeriya masu amfani da hidimar kamfanin, da kuma yin amfani da matsayinsa na mai jagora a kasuwa ta hanyar da ba ta dace ba.

Bisa duk wadannan kurakuran da kamfanin Meta ya aikata, hukumar kula da takarar kasuwanci da kare hakkin masu sayayya ta tarayyar Najeriya ta bukace shi da ya dauki matakan gyara daban daban, gami da yanke shawarar ci masa tarar dalar Amurka miliyan 220. (Bello Wang)