An kashe ‘yan aware masu dauke da makamai 4 a yankin masu magana da Turanci na Kamaru
2024-07-21 16:11:05 CMG Hausa
A kalla ‘yan aware hudu ne aka kashe a wani farmaki da sojoji suka kai yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru, yankin masu magana da harshen Turanci, a cewar sanarwar rundunar sojin kasar a ranar Asabar.
An kai harin ne a ranar Juma’a a unguwan Alabukam da ke Bamenda babban birnin yankin.
Sanarwar ta ce, a cikin wadanda aka kashe har da mataimakin kwamandan mayakan ‘yan aware na yankin wanda ke gallazawa fararen hula azaba.
Birnin Bamenda dai ya fuskanci sake barkewar tashin hankali tun farkon watan Yuli, bayan da mayakan ‘yan awaren suka ba da umarnin a yi wa dukkan motocin haya da ke birnin fentin launin shudi da fari, launukan tutar abin da suke kira “Ambazonia,” wanda suke son a kirkiro a yankunan masu magana da harshen Turanci na Kamaru wadanda ke a arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma.
A shekarar 2017 ne 'yan aware dauke da makamai suka fara artabu da dakarun gwamnati a yankunan. (Yahaya)