Mutane 22 sun mutu sanadiyyar rushewar wani gini a Nijeriya
2024-07-13 17:42:42 CMG Hausa
Mutane akalla 22 sun mutu yayin da wasu 132 suka jikkata, sanadiyyar rushewar ginin wata makaranta mai hawa biyu, da safiyar jiya Juma’a a jihar Plateau dake arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Ginin makarantar ta kudi da ta hada da firamare da sakandare a birnin Jos na jihar, ya rushe ne yayin da dalibai ke rubuta jarabawar shiga sabon aji.
Wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya, ta ruwaito kwamishinan yada labarai na jihar Musa Ashoms na cewa, zuwa yammacin jiyan, ma’aikatan ceto sun ceto jimilar mutane 154 daga karkashin baraguzan ginin, ciki har da gawarwaki 22 da wasu rayayyu 132, inda 6 daga cikinsu kuma ke cikin yanayi mai tsanani.
Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi mai tayar da hankali da ya samu jihar, inda ya bukaci ma’aikatan agaji su bincika cikin baraguzan ginin domin ceto karin mutane.
Cikin wata sanarwa kuma, shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin mai matukar tayar da hankali. (Fa’iza Mustapha)