Shugaban Guinea Bissau zai yi ziyarar aiki a Sin
2024-07-08 15:25:45 CMG Hausa
Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro El Mokhtar Sissoco Embalo zai kai ziyarar aiki a nan kasar Sin daga ran 9 zuwa 13 ga wannan wata, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ce ta sanar da hakan a yau Litinin. (Amina Xu)