Shugaban tarayyar Najeriya ya kaddamar da shirin samar da muhalli ga wadanda tashe-tashen hankula ya shafa
2024-07-07 16:24:48 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin kasa na samar da matsugunnai ga mutanen da suka rasa muhallan su sakamakon tashe-tashen hankula a wasu jahohin kasar.
Ya kaddamar da shirin ne a garin Tudun-Biri dake yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna ranar Juma`a 5 ga wata, inda ya yi kira ga al`ummar kasar da su hada kansu wajen yakar duk wani abu da ka iya zama barazana ga yanayin walwalar bil adama a kasa baki daya.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban na tarayyar Najeriya wanda mataimakin sa Sanata Kashim Shettima ya wakilta, ya jaddada aniyar gwamnati ta bunkasa kayayyakin aikin jami`an tsaro domin samun dauwamammen zaman lafiya, ya kuma kara da cewa shirin samar da mutsugunan an tsara aiwatar da shi ga al`ummomin jahohin Kaduna, Benue, Zamfara, Sakkwato da kuma jihar Kebbi, da zumma kwantar da hankulan mutanen da suka tsira da ransu sakamakon hare-haren ta`addanci a yankunan tare kuma da cire masu duk wata fargaba ta sake cin karo da irin wannan bala`i.
“Wannan shirin na tsugunar da mutane ba wai kawai ya tsaya ne kan jerin bulo da plasta ba kadai, dama ce da za mu hada kan mu wajen gina kasa, kana dama ce da ke bukatar kowa ya yunkuro domin yakar duk wani abu da ka iya zama barazana ga cigaban rayuwar mu”
A nasa jawabin, gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya yaba mutuka bisa yadda aka fara kaddamar da wannan shiri a jiharsa.
“Wannan ya nuna irin kokarin da shugaban kasa yake yi wajen tabbatar da ganin ya share hawayen al`ummar garin Tudun-Biri dama sauran al`umomin da suke da rauni a kasa baki daya”.(Garba Abdullahi Bagwai)