logo

HAUSA

Sama da mutane dubu 7 ne aka kashe a yammacin Afrika cikin watanni biyar kachal

2024-07-05 09:30:16 CMG Hausa

Ministan harkokin kasashen wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya yi kira ga kasashen dake cikin kungiyar Ecowas da su hada kansu domin shawo kan kalubalen tsaro da shiyyar ke fuskanta.

Ministan ya bukaci hakan ne a birnin Abuja ranar Laraba 3 ga wata cikin jawabin da ya gabatar yayin bude zaman na 52 na majalissar sasanci da harkokin tsaro na kungiyar Ecowas, ya jaddada muhimmancin daukar matakan bai daya wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda da na masu tsatsauran ra’ayi wadanda suke barazana ga zaman lafiya da kuma na ci gaban yankin.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan ya ce, kamar yadda bayanai suka nuna a tsakanin watan Janairu zuwa na Mayun 2024 sama da mutane dubu bakwai ne aka kashe a hare-hare dari takwas da ’yan ta’adda suka kai a wasu kasashe dake shiyyar, inda al’amarin ya fi kamari a kasashen Burkina Faso, da Niger da Mali.

Ministan wanda shi ne shugaban majalissar sasancin da tsaro na kungiyar Ecowas ya ce, a halin gaskiya babu yadda za a iya magance matsalolin ayyukan ’yan ta’adda ba tare da kowacce kasa dake cikin kungiyar ta Ecowas ta shigo ka’in da na’in ba.

Ya nanata bukatar karfafa hadin gwiwa da yin musayar bayanan sirri da kuma samar da wadatattun kudade da ayyukan rundunar hadin gwiwa na kungiyar Ecowas.

Ha’ila yau kuma ministan harkokin kasashen wajen na tarayyar Najeriya ya yi kiran da kara himmatuwa wajen shawo kan matsalolin da suka kama daga na sauyin yanayi, da yin kaura da rashin daidaito a bangaren tattalin arziki wanda yin hakan zai kawo kyakkyawan fata ga daukacin kasashen dake shiyyar.

Daga karshen Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya yabawa kungiyar ta Ecowas bisa hadin kai da take bayarwa a ayyukan zaman lafiya a kasashen Guine-Bissau da Gambia da kuma Saliyo. (Garba Abdullahi Bagwai)