logo

HAUSA

Jakadan Sin Dake Nijar Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar

2024-07-04 11:44:45 CMG Hausa

Jakadan Sin dake Nijar ya gana da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangaré a jiya Laraba, inda suka yi mu’ammala kan yadda ake share fagen taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka.

Jiang ya bayyana cewa, a watan Satumban bana, za a kira wannan taro a Beijing, inda za a samar da sabbin damammaki da bunkasuwa ga hadin gwiwar Sin da Afrika, ciki har da Sin da Nijar. Sin na fatan kara hadin gwiwa da Nijar, don tsai da manufofi a bangarori daban-daban, da kara bayyana karfin dandalin da gaggauta kafa kyakkyawar makomar Sin da Afirka ta bai daya zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, Sangaré ya ce, Nijar na jinjinawa kokarin da Sin take yi na shirya taron dandalin, wanda ya kasance wani gaggarumin biki ga zumuncin Sin da Afirka. Nijar na daukar taron da muhimmanci. Yana mai fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin wajen share fagen dandalin. Ya yi imani cewa, za a habaka hadin gwiwar kasashen biyu a dandalin, da ma ingiza huldarsu zuwa wani sabon mataki. (Amina Xu)