An kaddamar da aikin ginin hedikwatar hukumar raya shiyyar arewa maso gabas dake birnin Maiduguri
2024-06-20 09:09:49 CMG Hausa
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da aikin ginin hedikwatar din-din-din na hukumar raya yankunan shiyyar arewa maso gabashin kasar dake birnin Maiduguri.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da ofishin jiya Laraba 19 ga wata a Maiduguri, mataimakin shugaban kasar ya ce, kaddamar da aikin ginin yana daga cikin kokarin gwamnatin tarayya wajen zartar da matakan gaggawa da za su tabbatar da ci gaban shiyyar cikin hanzari.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Sanata Kashim Shettima ya ce, shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, yanki ne da yake matukar bukatar daukin gaggawa ta fuskoki da dama, kama daga batun ilimi, tsaro, samar da wadataccen abinci da kuma fadada kafofin aikin yi, bisa la’akari da yadda ta’addancin ’yan kungiyar Boko Haram ya yi mummunar tasiri a shiyyar.
Mataimakin shugaban kasar ha’ila yau ya ce, ofishin hukumar na din-din-din zai taimaka sosai wajen samun nasarar aiwatar da tsare-tsaren ci gaban yankin ta bangaren gina jama’a da bunkasar tattalin arziki karkashin mizanin dogo da matsakaici da kuma gajeren zango.
“’Yan Boko Haram dai sun aikata barnar da ta kai dalar Amurka biliyan tara a shiyyar arewa maso gabas. Jihar Borno kadai ta yi asarar da aka kiyasta ta kai ta dala biliyan 6.8 bayan dubban gidaje da suka lalata.”
Sanata Kashim Shettima wanda ya yabawa ’yan majalissar dokokin ta kasa da suka fito daga shiyyar saboda kokari da jajircewar da suka nuna har aka kai ga samar da ita wannan hukumar da za ta farfado da rushin shiyyar da ta rasa shekaru 10 da suka gabata sanadiyyar tashe-tashen hankali na ’yan kungiyar Boko Haram. (Garba Abdullahi Bagwai)