logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 80 a wani harin da suka kai ta sama

2024-06-19 09:48:34 CMG Hausa

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce a kalla 'yan ta'adda 80 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka tsere dauke da raunuka, sakamakon hare-haren sama da sojojin suka kai a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya a farkon makon nan.

Sojojin sun kai hare-haren ta sama a kan wuraren da 'yan ta'addan ke haduwa ne, a kauyen Gidan Kare da ke cikin karamar hukumar Faskare a jihar, a ranar Lahadin da ta gabata, a cewar kakakin rundunar sojin sama Edward Gabkwet, a wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a ranar Talata, a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.  .

Sama da babura 45 na 'yan ta'addan ne aka kona a yayin farmakin. Kafin a kai farmakin ta sama, rundunar sojin ta samu sahihin bayanan sirri na cewa 'yan ta'addan da yawansu ya haura 100, sun kona gidaje a wani kauye mai tazarar kilomita biyar daga kauyen Gidan Kare. (Yahaya)