logo

HAUSA

Bututun mai: An yankewa ’yan Nijar uku hukuncin zaman kason watanni 18 tare da jinkirta tuhumar

2024-06-18 10:48:03 CMG Hausa

A ranar jiya Litinin 17 ga watan Junin shekarar 2024, kotun yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa, da yaki da ta’addanci CRIET dake birnin Cotonou na kasar Benin ta yankewa ’yan Nijar din uku na kamfanin WACPO-Niger hukuncin zaman kason watanni 18 tare da jinkirta tuhumar.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

Ita dai wannan shari’a ta fara wajen karfe goma na safe, kuma daga cikin wadannan ’yan Nijar uku da suka bayyana a gaban mambobin kotun CRIET, madam Moumouni Hadiza Ibra, mataimakiyar shugaban WACPO-Niger, ita ce ta fara bayyana sannan Ismael Cisse Ibrahim da Massoubaou Dan Kane dukkansu sufetocin man fetur. Gaban alkalan kotun CRIET, ’yan Nijar din uku sun yi watsi da tuhumar da ake musu, tare da bayyana cewa ba su aikata laifin kome ba, sun zo Benin bisa aikin da ya kamata su yi tare da takwarorinsu na WACPO-Benin.

A karshen wannan zaman kotu, an yankewa wadannan ’yan uku hukuncin daurin watanni 18 a gidan yari tare da jinkirta tuhumar.

Ku rike cewa tun yau da kusan ’yan makwanni, ake tsare da wadannan ’yan Nijar uku a kasar Benin, bayan da kotun CRIET ta tuhume su da manyan laifuka biyu, da suka hada da shiga kasar Benin ba bisa ka’ida ba da kuma gabatar da katin shaidar aiki ta jabu.

A halin yanzu, tare da wannan hukunci, wadannan ’yan Nijar uku sun samu walwala, kuma alkalin shari’a ya ba da umurnin da maida musu kayayyakinsu da aka karbe. Ana sa ran su iso gida Nijar nan bada jimawa ba.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.