logo

HAUSA

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta UNHCR ta yi kira ga kasa da kasa domin magance matsalar jin kai a yankin Sahel

2024-06-13 13:42:38 CMG Hausa

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta UNHCR ta bayyana damuwa kan matsalar jin kai da ke kamari a yankin Sahel. Bisa ga alkaluman watan Afrilun shekarar 2024, fiye da mutane miliyan 3.3 tashe tashen hankali suka talistawa barin muhallinsu a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Rahoton na HCR na cewa baya ga dalilan da ke haddasa ci gaban tashe tashen hankali, illolin sauyin yanayi na kara tsananta halin da ake ciki. Wannan adadin fararen hula da aka tilastawa barin wurarensu, na bukatar wata hadakar kasa da kasa cikin gaggawa domin kaucewa karin matsaloli.

A cewar UNHCR, mutane miliyan 2.8 suka gudu daga muhallinsu na cikin gida a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar a tsawon shekaru 4 na baya bayan nan, haka kuma, adadin ‘yan gudun hijira na wadannan kasashe ya zarce mutane dubu 550 a daidai lokaci guda.

A shekarar da ta gabata, adadin ‘yan gudun hijirar Burkina Faso, ya karu da kimanin mutane dubu 117 da dari 6 wadanda kuma suka isa kasashe makwabta na bakin teku a cewar binciken watan Afrilun shekarar 2024.

A yanzu haka, akwai ‘yan gudun hijirar Mali dubu 200 da ke Mauritaniya, dubu 130 a Nijar, kusan dubu 40 a Burkina Faso, da wasu dubu 50 da suka isa Aljeriya. A yayin da ‘yan gudun hijira dubu 94 da suka fito daga kasashen Burkina Faso, Nijar da Mauritaniya suke zaune a kasar Mali. A yayin wannan kasa kuma take fama da mutanen da suka kaura na cikin gida fiye da dubu 354.

A cewar, rahoton, UNHCR na bukatar dalar Amurka miliyan 443.5 domin amsa bukatun jin kai na gaggawa a Burkina Faso, Mali, Nijar, Mauritaniya da kuma kasashen yankin Golf din Guinee.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyar Nijar.