logo

HAUSA

Ana gudanar da bincike domin gano jirgin Malawi da ya bace dauke da mataimakin shugaban kasar

2024-06-11 10:17:19 CMG Hausa

Ana gudanar da bincike a Malawi, don gano jirgin sama da ya bace dauke da mataimakin shugaban kasar, Saulos Chilima tare da wasu mutane 9.

Jirgin mallakin rundunar sojin kasar, ya bace ne da safiyar jiya Litinin, kuma bai sauka a inda ya nufa ba wato filin jirgin saman Mzuzu dake yankin arewacin kasar, inda mataimakin shugaban ya kamata ya sauka don halartar jana’izzar tsohon atoney-janar, kana ministan shari’a na kasar, Ralph Kasambara.

Rundunar soji da ta ’yan sandan Malawi, tare da sauran hukumomin tsaron kasar, na gudanar da bincike a dajin Chikangawa dake wajen birnin Mzuzu, inda ake zaton jirgin ya bace. (Fa’iza Mustapha)