logo

HAUSA

MDD: Kusan mutane miliyan 33 a Sahel na bukatar agajin ceton rai da kariya

2024-06-08 16:29:48 CMG Hausa

Ma’aikatan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana a ranar Juma’a cewa, mutane miliyan 32.8 a yankin Sahel na Afirka wadanda suka fito daga kasar Senegal zuwa kasar Eritrea, suna bukatar agajin gaggawa da kariya.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD wato OCHA a takaice, ya sanya wannan gargadin a cikin takaitaccen bayani kan bukatun yankin Sahel na shekarar 2024, inda ya bayyana cewa, a yankin na Sahel, tashin hankali da rikice-rikice na barazana ga rayuwa da bukatun rayuwa, lamarin da ke tilastawa iyalai kauracewa gidajensu tare da hana su samun ababen more rayuwa na asali. Yara miliyan 2.2 ne ake tauye musu hakkinsu na samun ilimi sakamakon rufe makarantu, kuma an rufe kusan cibiyoyin kiwon lafiya 1,300.

MDD da abokan huldarta na bukatar dalar Amurka biliyan 4.7 a bana don tallafawa mutane miliyan 21 a Burkina Faso, da yankin arewa mai nisa na Kamaru, Chadi, Mali, Nijar, da jihohin Adamawa, Borno da Yobe na Najeriya. Ya zuwa yanzu, kashi 16 cikin 100 na kudaden, ko kuma dala miliyan 761 ne aka samu. (Yahaya)