logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya bukaci a kara samar da dabarun zubawa nahiyar Afrika jari

2024-06-07 10:45:55 CMG Hausa

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya bukaci masu zuba jari ga ayyukan raya kasashe na duniya, su dauki nahiyar Afrika a matsayin wurin samun ci gaba da wadata, yana mai kira gare su da su kara samar da dabarun zuba jari a bangarorin aikin gona da ababen more rayuwa da bincike da samar da ci gaba.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da wata tawagar kamfanin zuba jari na kasa da kasa (IFC), wanda mamba ne na Rukunin Bankin Duniya, da ta ziyarce shi a Abuja babban birnin Nijeriya, karkashin jagorancin manajan daraktan kamfanin, Makhtar Diop.

Shugaban na Nijeriya ya nanata cewa, Afrika na da karfin samun ci gaba da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da wadata, yana mai cewa, ya kamata duniya ta rika ganin nahiyar a matsayin wadda za ta iya taimakawa sauran sassan duniya, ba wai a matsayin koma baya, mai rashin zaman lafiya, da matsalolin shugabanci ba. (Fa’iza Mustapha)