logo

HAUSA

Kungiyar matasan Philippines masu wasan tseren kwale kwale na “Dragon Boat” sun cimma burin shiga babbar gasar kasar Sin

2024-06-06 15:41:46 CRI

Lokacin da matashi Ronen Estoque mai shekaru 18 da haihuwa daga kasar Philippines, ya kammala wasan share fage na tseren kwale-kwale a gasar wasannin 2024 ta Sin da kasashen kungiyar ASEAN, ko “China-ASEAN Dragon Boat Open”, ya gamsu sosai da kwazon kungiyar wasan ta kasar Sin.

A cewar Ronen Estoque, "Suna da karfi da sauri. Na san a nan kasar Sin aka yanke cibiyar wasan tseren kwale-kwale na “dragon boat”, don haka zuwan mu nan, da shiga gasar wata dama ce gare mu ta yin musaya".

An bude gasar ta “China-ASEAN Dragon Boat” ta bana ne a karshen makon jiya a birnin Wuzhou, na lardin Guangxi na kudancin kasar Sin, kuma kungiyoyi 28 ne suka shiga gasar, ciki har da guda 4 daga kasashe mambobin kungiyar ASEAN, inda aka gudanar da gasar cikin kwanaki 2.

A matsayin sa na matashi mai wasan na tseren kwale kwale karkashin kungiyar Brgy Carmen daga birnin Cagayan de Oro na kasar Philippines, Estoque ya shafe shekaru 2 yana yin horo, kuma wannan ne karon farko da ya shiga gasar kasa da kasa.

Estoque ya lura cewa ya kamu da kaunar wasan tseren kwale kwale tun yana karami, kasancewar ya tashi ne a cikin iyali dake yin wasan. Mahaifiyarsa tana cikin kungiyar masu wasan tseren kwale kwale ajin mata, kuma dan uwansa, da ‘yar uwarsa ma suna yin wasan a Philippines.

Da yake tsokaci game wasan, Sunny Raed Cahayag, jagoran kungiyar Brgy Carmen Dragon, ya ce "Sin ita ce tushen wasan tseren kwale kwale na “dragon boat”, don haka zuwan mu kasar Sin domin shiga gasar tseren kwale kwale wani mafarki ne da ya cika ga matasan ‘yan wasan mu. Mun kafa wannan kungiya ne tun a shekarar 2022, kuma dukkanin ‘yan wasan mu dalibai ne. Wannan ne karon farko da matasan ‘yan wasan mu suka fita daga Philippines domin shiga wata gasa. Gasar ta ba mu damar haduwa da ‘yan wasa na manyan kungiyoyin wasan tseren kwale kwale inda muka samu karin kwarewa".

Cagayan de Oro birni ne dake tashar teku a kasar Philippines. Kuma dunkulewar al’adun Sin da na Philippine ya yi tasiri, tare da samar da yanayi na musamman na al’ummar Sin dake wurin, kuma wasan tseren kwale kwale ya zama wasa dake ta kara karbuwa a wurin.

A ganin Cahayag, duk da cewa wasa ne ba wanda ake yin sa a ko ina ba, wasan tseren kwale kwale na “dragon boat”, ya yi matukar yaduwa cikin sauri a wurin, kuma akwai kungiyoyin wasan masu yawa a birnin na Cagayan de Oro. 

Suhod Hakim, coki ne a kungiyar Brgy Carmen Dragon, kuma wanda ya taba wasa, ya kuma horas da kungiyar kasar Philippines ta wasan. Ya ce "Iyali na suka birnin Manila fadar mulkin Philippines. Na zo nan birnin Cagayan de Oro City domin horas da ‘yan wasa, saboda yaran suna matukar son wasan tseren kwale kwale. Suna tashi daga bacci tun karfe 4:30 na safe domin yin atisaye na sama da sa’o’i 2 kafin su tafi makaranta. Akwai birbishin al’adun kasar Sin a birane da yawa na kasar Philippine. Akwai wuraren cin abinci, kuma bikin bazara na kasar Sin na kara yaduwa a wurin, saboda tasirin da al’adun kasar Sin ke kara yi a Philippines. Na taba zuwa Nanning sau biyu inda na shiga gasar tseren kwale kwale ta “dragon boat”. Kaza lika na je biranen Guangdong, da Shanghai, da Zhejiang da wasu karin wuraren. Irin wadannan gasanni ba kawai suna taimawa ‘yan wasa wajen bunkasa matakin shiga gasanni ta hanyar musaya ba ne, har da ma taimakawa al’ummun kasashen biyu da damar bunkasa cudanya, da musaya tsakanin jama’ar su".