logo

HAUSA

An yi nasarar turke na’urar Chang'e-6 a falakin duniyar wata dauke da samfuran da aka debo daga bangaren wata mai nisa

2024-06-06 21:01:13 CMG Hausa

 

Da karfe 3 sauran mintuna 12 na yammacin yau Alhamis, bisa agogon Beijing ne sashen na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-6 da ya tashi daga duniyar wata mai nisa, ya cimma nasarar hadewa da sassa 2 na’urar, a falakin da ke kewayen duniyar wata.

Hukumar kula da harkokin zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar ko CNSA ta tabbatar da hakan, inda ta ce, da karfe 3 da mintuna 24 na yammacin yau din, an yi nasarar sanya mazubin dake kunshe da samfuran daga bangaren wata mai nisa irinsu na farko a duniya, cikin sashen na’urar da zai sauko da su doron duniya.

Ana sa ran sashen na’urar da zai dawo doron duniya, zai sauka dauke da samfuran bangaren duniyar wata mai nisa, a yankin Siziwang Banner, na jihar Mongoliya ta Gida mai cin gashin kai, kamar dai yadda aka riga aka tsara.   (Saminu Alhassan)