logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kaduna tare da hadin gwiwa da kamfanin ’yan kasuwar kasar Sin sun kaddamar da masana’antar sarrafa sinadarin Litiyom

2024-06-06 09:15:39 CMG Hausa

An kaddamar da kashin farko a kamfanin sarrafa sinadarin Litiyom a garin Kangimi dake yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda za a rinka samar da tan 1,500 a kullum.

A lokacin da yake kaddamar da kamfanin a karshen mako jiya, a ci gaba da bikin cikarsa shekara guda a kan mulki, gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya ce, kamfanin na kasar Sin Ming Xing Separation Nig. Ltd yana da kaso 70 na jari a masana’antar yayin da gwamnatin jihar kuma ke da kaso 30.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Sanata Uba Sani ya ce, adadin dala miliyan 20 aka kashe wajen kammala kashin farko na kamfanin, wanda ake sa ran kuma zai samar da guraben aiki har dubu 3 a bangaren hakar ma’adanin da kuma bangaren aikin sarrafa ma’adanin.

Ya ce a yanzu haka dai jarin da aka saka na iya dala miliyan 20 ne, amma akwai shirin karawa zuwa miliyan 50 nan da shekara daya.

“Kamfanin na Ming Xing Separation Nig. Ltd yana da shirin samar da kamfanin kayayyakin samar da tiles, inda za a rinka amfani da wani bangare na sinadaran Litiyon, wanda hakan kuma zai kara bayar da damar wasu karin guraben aiki guda dari 5, kuma sun yi alkawarin gayyato wasu kamfanonin zuwa jihar ta Kaduna domin saka jarinsu saboda kyakkyawan yanayin da gwamnatin jihar ta samar.”

A jawabinta, wakiliyar kamfanin Mrs Liana Li yabawa ta yi matuka bisa irin hadin kai da gwamnatin jihar ta Kaduna ta ba su, har suka kai ga samun nasarar assasa kashin farko na kamfanin a garin na Kangimi.

“Ina son na tabbatar muku cewa, ayyukanmu za su kasance bisa tsarin da duniya ke amfani da shi, kuma za mu kiyaye da dokokin kasa.” (Garba Abdullahi Bagwai)