logo

HAUSA

Matakan Amurka na nuna bambanci ga motoci kirar Sin masu amfani da lantarki a karshe za su illata ita kanta Amurkan

2024-06-06 20:42:04 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin tana samar da kudin tallafi ga wasu sana’o’i ne bisa ka’idojin hukumar cinikayya ta duniya wato WTO, tare da mutunta ka’idojin yin adalci, da rashin nuna bambanci kuma ba tare da boye kome ba. Ba ta saba ka’idojin hukumar WTO a fannin ba da kudin tallafi ba.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana a yayin da yake hira da wakilin mujallar Times cewa, gwamnatin kasar Sin ta bayar da kudin tallafi masu yawa ga kamfanonin kera motoci masu amfani da lantarki, don sa kaimi ga shigar da su kasuwannin Amurka, kuma hakan ne ya sa Amurka ta mayar da martani.

Game da wannan batu, Mao Ning ta ce, kayayyakin Sin masu amfani da sabbin makamashi, ciki har da motoci masu amfani da wutar lantarki, sun samu karbuwa sosai a kasuwannin kasa da kasa, domin ana samar da su ne ta hanyoyin kirkire-kirkire, da raya tsarin sayar da su, da kuma samun fifiko a kasuwannin kasa da kasa.

Ta ce, kamfanonin Sin sun yi kokari, tare da samun sakamako, ba wai saboda samun kudin tallafi daga gwamnati ba. A shekarar bara, Sin ta fitar da motoci masu amfani da lantarki dubu 13 ne kacal zuwa Amurka, don haka ba su yi yawan da Amurka ke zuzutawa ba. (Zainab Zhang)